20 Disamba 2021 - 16:24
Ana ci Gaba Da Gudanar Da Taron Kungiyar OIC Karo Na 17 A Pakistan

Tuni ministocin harkokin wajen kungiyar Hadakan kasashen Musulmi OIC suka hallara a birnin Islamabad na kasar Pakistan domin halartar taro a babban dakin taro na majalisar dokokin kasar dake birnin Islam Abad na kasar Pakistan inda za’a tattauna game da halin da kasar ta Afghanistan ke ciki,bayan ficewarwa sojojin Amurka da kuma karbe ragamar mulkin kasar da kungiyar Taliban ta yi.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - An bude taron ne da jawabi daga bakin sakatare Janar din kungiyar ta OIC wato Minsitocin harkokin wajen kasar Saudiya da kuma Pakistan , kuma ana saran ministan harkokin wajen kasar Iran Amir Abadallahiyan dake jagurantar tawagar kasar awajen taron zai gabatar da jawabi ,

A wani bayani day a wallafa a shafinsa na twita gabanin fara taron Fira ministen Pakistan Imran Khan ya fadi cewa makasudin gudanar da taron gaggawan shi ne domin nuna goyon bayan alummar Afghanistan da kuma lalubo hanyoyin da za’a bi wajen taimaka ta warware matsalar jin kai da take fuskanta.

342/